Kimiya da fasaha: Ana kera jirgin ruwa mai amfani da wutan lantarki zalla

Kimiya da fasaha: Ana kera jirgin ruwa mai amfani da wutan lantarki zalla

- kamfanin Rolf Sandvik zai kera wani katafaren jirgin ruwa wanda zai rika amfani da wutan lantarki zalla ba tare da wani inji ba

- Za a kammala keran wannan jirgin ne a watan Afrilu na shekara 2018 wanda zai iya kwasar fasinjoji 400

- Kamfanin ta ce jirgin zai rage gurbatar muhalli

Wani kamfani a kasar Norway ya ce yana kera wani katafaren jirgin ruwa da ya yi amannar cewa shi ne irinsa na farko da zai rika amfani da wutan lantarki zalla ba tare da wani inji na ko-ta-kwana ba.

Jirgin ruwan da ba zai rika fitar da hayaki ko kadan ba, idan an kammala shi a watan Afrilu mai zuwa zai iya kwasar fasinjoji 400 a yammacin Norway.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, shugaban kamfanin Rolf Sandvik ya bayyana cewa jirgin zai rage gurbatar muhalli, a wani yanki da hukumar raya Ilmi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta ware.

Kimiya da fasaha: Ana kera jirgin ruwa mai amfani da wutan lantarki zalla
Jirgin ruwa mai amfani da wutan lantarki zalla

KU KARANTA: Kasafin kudin 2017: Yadda Ministocin Buhari su ka hana Osinbajo sa hannu

Ya kara da cewa yana fatan a matsayin shi na dan kasuwa, nan gaba shugaba Trump na kasar Amurka wata rana zai fahimci cewa akwai matukar tasiri ta fuskar kasuwanci a rika daukar batun kula da yanayi da matukar muhimmanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan jirgin sama da aka kera a Najeriya zai tashi kuwa?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng