Sabo da kaza: Damisa ta kashe mai kula da namun daji

Sabo da kaza: Damisa ta kashe mai kula da namun daji

- Matar ta mutu ne sakamakon firgice data shiga a lokacin da tayi arba da damisa

- Damisar ta balle ne daga kejinta

Wata mata dake mai kula da namun daji dake ajiye a gandun dajin Hamerton na kasar Ingila, Rosa King ta mutu sakamakon rikicewa bayan wata damusa ta shiga wani kewaye da take ciki.

Matar mai shekara 33, ta mutu ne sakamakon firgice data shiga a lokacin da tayi arba da damisar, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

KU KARANTA: Badaƙalar naira biliyan 24: An cigaba da cacar baki tsakanin El-Rufai da Jonathan

Hukumar Yansandan Cambridgeshire tace: "Wata Damisa ce ta ɓalle daga kejin ta, inda ta shiga wani kewaye wanda ita matar mai kula da namun dajin take ciki a wannan lokaci. Kuma sai abin ya zo da ƙarar kwana, matar ta mutu a bayin."

Sabo da kaza: Damisa ta kashe mai kula da namun daji
Damisa

Sai dai nan da nan aka fitar da dukkanin masu ziyarar yawon bude ido daga gandun namun dajin, sa’annan Yansandan sun ce ba’a san lokacin da damisar ta fice daga kewayen ba.

Suma a nasu bangaren, hukumar gandun namun dajin na Hamerton ta fitar da wata sanarwa inda take cewa: "Bisa dukkan alamu wannan lamari ya auku ne sakamakon halin tsananin firgici da rudu da matar ta shiga.

"Don haka muna matuƙar juyayi da taya abokan aiki, yan'uwa da abokan arziki alhinin rashin wannan mata, sa’annan zamu gudanar da bincike kan wannan lamari”

Daya daga cikin amsu kawo ziyarar bude ido a gandun dabbobin yace: "Mun kusa zuwa kewayen damusar sai wani mai kula da namun dajin ya ƙwalla mana kira cewa duk mu yi sauri mu fita."

Maijiyar Legit.ng ta bayyana a shekarar 1990, aka bude gandun namun dajin, kimanin shekaru 27 kenan da suka gabata, kuma damusoshi da dama da aka samo daga ƙasar Malaysia da Bangladesh, har ma da dabbobi irin su kyarkeci da dila akwai a dajin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana bukatar sabbin shuwagabanni a kasar nan:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng