Sirrin da ke tattare da cin danyen tumatir musamman ga mai Azumi
Wani dalibi a jami’ar Maiduguri mai suna Jesse Tafida ya binciko wadansu hanyoyi da za a iya amfani da danyen tumatir wajen karfafa garkuwar jika da samar wa jiki lafiyar da take bukata, da kuma amfanin da ke gareshi a jikin dan Adam musamman yanzu da musulmai ke azumin watan Ramadan.
Ya ce ya gano hakan ne bayan binciken da ya gudanar akan sinadarorin da dayen tumatir ke dauke da su da mutane da yawa basu sani ba.
Legit.ng ta samu labarin cewa Tafida ya gano cewa tumatir na dauke da sunadarin da ake kira ‘Antioxidants’ a turance da ke kare mutum daga kamuwa daga wasu cututtuka sannan kuma ana samun sinadarin Vitamins A da B da kuma Folic Acid a cikinsa.
Dalibin yace cin dayen tumatir na kare mutum daga kamuwa da cutar daji, hawan jini da kuma bugawar zuciya.
Ya ce wasu binciken sun nuna cewa idan ana gauraya danyen tumatir a cikin abinci musamman cikin wasu gaiyayyakin da ake ci kamar zogale, rama da makamatansu yana rage cutar siga.
Ya kuma ce za a iya cin dayen tumatir idan cikin mutum ya murde ko kuma idan cikin mutum na ciwo sannan yana kuma rage kiba a jiki musamman ga wadanda suke bukatar haka.
Tafida ya ce cin dayen tumatir na kara karfin ido da kuma ya kare idon daga kamuwa daga wasu cututtuka kamar yanar ido, amosanin ido da makamatan su.
Daga karshe ya shawarci matan da suke dauke da juna biyu da su yawaita cin dayen tumatir lokacin da suke da ciki da kuma bayan sun haihu domin yana taimakawa wajen kare jariri daga kamuwa da cututtuka da kuma taimaka masa wajen girma.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng