Ramadan: Munanan dabi'u 4 da musulmai ya kamata su kaurace mawa

Ramadan: Munanan dabi'u 4 da musulmai ya kamata su kaurace mawa

- Shafukan sada zumunta da muhawara na zamani wata hanya ce da al’umma ke amfani da ita domin cimma bukatu daban-daban.

- Wasu na neman ilimi, wasu kasuwanci, wasu kuwa na yin amfani da su ne domin watsa labaran karya da kuma cin zarafin jama’a.

Majiyar mu ta tattauna da Malam Musa Sani, limamin daya daga cikin masallatan rukunin gidaje na Efab da ke Abuja, babban birnin Najeriya, kuma ya yi mana karin bayani akan abubuwan da ya kamata mutum ya kiyaye don amfani da wadannan shafuka musamman ma a lokutan azumi.

1. Karya

Karya na cikin manyan abubuwan da addinin Musulunci ke Kyamar su.

Ayoyi da dama a cikin Al-Kur’ani mai tsarki sun yi gargaɗi a kan karya, inda suke bayyana irin azabar da Allah ya tanadarwa makaryata.

Kazalika, hadisai da dama sun bayyana makaryata a matsayin mutanen da ba a bukatar azuminsu.

Misali, wani hadisi da Abu Huraira ya rawaito ya ambato Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:

“Duk mutumin da bai daina karya ba, Allah ba ya bukatar sa da ya daina cin abinci ko shan abin sha (wato Allah ba zai karbi azuminsa ba.)”.

Ramadan: Munanan dabi'u 4 da musulmai ya kamata su kaurace mawa
Ramadan: Munanan dabi'u 4 da musulmai ya kamata su kaurace mawa

2. Yada jita-jita

Masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara sun yi fice wajen yada jita-jita, lamarin da sau da dama kan haifar da mummunan sakamako.

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce, “Ya ishi mutum zunubi a ce duk labarin da ya ji sai ya yada shi.”

3. Batsa

Hotuna da bidiyo da kuma kalaman batsa na daga cikin abubuwan da suka mamaye shafukan sada zumunta da muhawara.

Haka kawai, babu kunya, za ka ga masu amfani da shafukan suna sanya batsa, kuma suna yin tsokaci a kansu.

Yawancin lokuta ma sukan tura su ga abokansu da ke shafukan, ko da kuwa ba su nemi a tura musu ba.

Hakan yakan fusata mutane da dama.

Ramadan: Munanan dabi'u 4 da musulmai ya kamata su kaurace mawa
Ramadan: Munanan dabi'u 4 da musulmai ya kamata su kaurace mawa

4. Jin kade-kade

Jin kade-kade da wake-wake na cikin abubuwan da aka yi hani da su a Addinin Musulunci idan ba a wasu lokutan kebabbu ba, musamman inda aka amince mata su yi kida da waka a lokutan biki.

Ko su ma ba a yarda su bayyana al’aurarsu a lokacin da suke waka ba.

Don haka masu amfani da shafukan zumunta na zamani su guji fadawa irin wannan tarko, ganin yadda shafin intanet ya cika makil da kade-kade da wake-wake Wadanda wasunsu ma na batsa ne.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng