Markadaddun ababen sha kala 5 masu kayatarwa da kara lafiya a jikin dan adam

Markadaddun ababen sha kala 5 masu kayatarwa da kara lafiya a jikin dan adam

- Markadadun abin sha wadanda a turance a ke kiran su smoothies ana yin su ne da kayan itace kala kala ko kuma kayan lambu.

- Banbancin su da abin sha da muka sani shine su ba ruwan ake tacewa ba, gaba daya ake markade su.

- Wannan ya sa amfanin su a jiki ke zuwa a ribanye, ban da dadin da suke da shi kamar kunne ya fita.

Legit.ng ta zakulo maku daga kafar labarai ta Al'umma wasu markadadun abin sha kala 5 domin ku kara kayata Iftar din ku:

1. Tuffa da Ayaba

Bayan an bare ayabar, yayyanka su kawai za a yi, a markade su da injin markade. Zaa iya kara kankara a nikan idan ba za a saka shi a fridge ya yi sanyi ba.

2. Abarba da gurji

Ba sai an fere Gurjin ba, Abarbar dai za a fere ta a cire baki bakin ta sannan a yayyanka su a markada.

Markadaddun ababen sha kala 5 masu kayatarwa da kara lafiya a jikin dan adam
Markadaddun ababen sha kala 5 masu kayatarwa da kara lafiya a jikin dan adam

3. Gwanda da kwakwa

Za a gyara gwanda wacce ta nuna, a yanke bawon sannan a cire ‘ya’yan, a fasa kwakwa a bambare ta amma ba sai an kankare bawon ta ba. A yayyanka su a markada.

4. Piya (Avocado) da Ayaba

Bare su kawai za a yi a markada.

Markadaddun ababen sha kala 5 masu kayatarwa da kara lafiya a jikin dan adam
Markadaddun ababen sha kala 5 masu kayatarwa da kara lafiya a jikin dan adam

5. Kankana da Abarba

Za a gyara Abarbar, kamar yadda na fada a baya, a cire har itacen tsakiyar, sannan a yanka Kankanar, a cire ‘ya’yan (amma idan abin markaden mai kyau ne za a iya markadawa har ‘ya’yan).

Kar a manta a kowannen su za a iya zuba kankara kafin a markada, sannan za a iya kara kayan kamshi da nono, duk yadda dai za a yi a kara ma shi armashi.

Sannan a sani wannan kawai somin tabi ne na bayar, za a iya hada kayan itatuwa daban daban ba lallai sai biyu ba kawai.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel