Sabuwar doka: An haramta sakin aure a watan Ramadan a wata ƙasar Larabawa
- Wani alkalin a kasar Falasdin ya haramta sakin aure a watan Ramadan
- Alkalin yace ba zai saurai kara daya danganci mutuwar aure ba har sai bayan watan Ramadan
Wani alkalin a kasar Falasdin ya haramta sakin aure a watan Azumin Ramadan mai alfarm, inda alkalin yace saboda yunwa ya kan sa wasu mazajen su saki matayensu.
Alkali Mahmoud Al-Habbash, shugaban kotun shari’ar musulunci na kasar Falasdin yace sakamakon Azumi na hana ma mutane cin abinci ko shan sigari da rana, hakan ya kai wasu ga aikata abin da zasu dawo suna nadama.
KU KARANTA: Gidan sama hawa 3 ya ruguje a jihar Legas, rayuwaka da dama sun salwanta
Don haka alkalin yace ba zai saurai kowanne irin kara daya danganci mutuwar aure ba har sai bayan watan Ramadan, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
A tsarin kasar Falasdin, Kotunan musulunci kadai ke da daman raba aure. Hukumomin kasar sun bayyana a shekarar 2015 an samu sabbin aure sama da 50,000, amma kuma a cikinsu aure 8000 sun mutu.
Idan ba’a manta ba Legit.ng ta ruwaito fara azumin watan Ramadan a Najeriya tun a ranar Asabar din data gabata, inda ake bukatar musulmai su kaurace ma saduwa, cin abinci, shaye shaye da sauransu har sai rana ta fadi.
Daga karshe bayan kwanakin watan sun kare sai a gudanar da Sallah karama, inda yawanci ake kwashe kwanaki 3 ana gudanar da shagulgulan sallan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda ake yi wa yan Najeriya dauki dai dai a kasar Sin
Asali: Legit.ng