Wani dan majalisa ya raba kaya na kimanin milyan 150 ga al'ummar mazabarsa (Hotuna)
- Honorabul Abdullahi Idris Garba ya tallafa wa Al'ummar Mazabarsa da kayayyakin aiki domin taimakawa kansu
- Honorabul ya bada wannan tallafi ne ganin halin da al'ummar kasar ke ciki na rashin abun yi musamman al’ummar mazabarsa
- Wannan tallafin ba shine karon farko ba, domin ko shekarar da ta gabata ya bada tallafi makamancin haka ga al’ummarsa
A kokarin sa na ganin ya farantawa al'ummar sa rai tare da tallafa masu akan yadda zasu dogara da kan su, a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu ne Honorabul Abdullahi Idris Garba (Maisola) dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kontagora, Mariga, Mashegu da Wushishi dake jihar Neja ya raba kayayakin da suka hada da keke napep guda 35, babura guda 45, firijin na sanyaya ruwa guda 45, kananan taraktocin hannu nazamani guda 10 da injin nika guda 90 da injimin gyaran gashi ga mata masu sana'ar gyaran gashi guda 25 da kilipa ga masu sana'ar aski na zamani guda 50, duk da zummar tallafa masu domin su bunkasa sana'o'in su.
Honarabul Maisola ya bayyana cewar: “Ya yi wannan shiri naba da tallafi ne ganin halin da al'ummar kasar nan ke ciki na rashin abun yi da kuma fatara ya yi wa al'umma yawa wanda ina da kyakkyawan zaton hakan zai rage masu radadin talaucin da ake fama da shi a kasa.”
Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin, dan majalisar ya kuma yi kira ga wadanda suka samu wandan nan kyaututtuka da su yi amfani da shi kamar yadda ya dace domin taimakawa kansu har su taimakawa 'yan uwansu, ya kuma baiwa wadanda ba su samu wannan tallafi ba hakuri, inda ya kara da cewa wata rana su ma rabon su na nan tafe.
KU KARANTA: AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu (HOTUNA)
Da daman wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi ne suka nuna matukar godiyan su tare da addu'ar Allah ya saka masa da alkairi, sun kuma yi kira ga sauran zababbun wakilai da shugabanni da su yi koyi da wannan dan majalisa wurin ganin sun tallafawa al'ummar su domin ciyar da wannan kasar gaba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan dan majalisa ke gudanar da irin wannan shiri na bada tallafi ga al'ummar sa ba, domin ko shekarar da ta gabata ya bada tallafi makamancin haka ga al'ummar mazabar tasa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa
Asali: Legit.ng