INNA LILLAHI WA'INNA ILLAIHI RAJU'UN: Tsohon gwamnan Jihar Gombe Kanal Muhammad Inuwa Bawa ya rasu
- Yau ranar juma’a Allah ya yi wa Kanal Muhammad Inuwa Bawa mai ritaya rasuwa
- Marigayin ya yi gwamnan jihohin Ekiti da Gombe na zamanin mulkin soja na marigayi janar Sani Abacha
- Bawa ya rasu ne a wani asibiti a garin Jos baban birnin Jihar Filato
Allah ya yi wa Kanal Muhammad Inuwa Bawa mai ritaya tsohon gwamnan jihar Gombe na zamanin mulkin soja rasuwa .
Legit.ng ta ruwaito cewa, Inuwa Bawa dai ya shine gwamnan jihar Ekiti na farko daga watan Oktoba 1996 zuwa Agusta 1998 kuma ya kasance gwamnan jihar Gombe na biyu bayan samun Jihar duk a zamanin mulkin soja na marigayi janar Sani Abacha daga watan Agusta 1998 zuwa Mayu 1999.
KU KARANTA: Kotu ta hana El-Rufai rusa kasuwar barci
Kanal Bawa yana shekaru 63 da haihuwa, ya rasu ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Mayu wato yau a wani asibiti a garin Jos baban birnin Jihar Filato, bayan yi masa tiyata, yadda rahotanni ta ce.
Allah Ya jikan sa da rahama .
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari
Asali: Legit.ng