Bikin ranar yara ta duniya

Bikin ranar yara ta duniya

- A ranar Asabar 27 Mayu ne ranar yara ta duniya

- Yaran talakawan Najeriya na fuskantar kalubale game da kiwon lafiyarsu

- An shawarci gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali wajen magance kalubale da yaran talakawa ke fuskanta a harkokin kiwon lafiya

Ranar 27 ga watan Mayu na kowace shekara ne aka ware don bikin ranar yara a duk faɗin duniya ba tare da la'akari da bambance-bambance kabila, launi, aqidar, addini da sauransu ba.

A ranar Asabar, 27 ga watan Mayu wato gobe ke nan bikin ranar yara na wannan shekara zai zagayo. Duk da haka, abin tambaya a nan shine, yaya kiwon lafiyar yaran talakawan Najeriya idan aka kwatanta da sauran na duniya?

Ba sabuwar abu bane cewa yaran talakawan Najeriya na fuskantar kalubale na rashin kulawa da kiwon lafiyarsu. Najeriya na fuskanta kalubale daban-daban kankiwon lafiyar yara.

Bikin ranar yara ta duniya
A ranar Asabar 27 Mayu ne ranar yara ta duniya

Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin naijaloveinfo cewa kan harkokin kiwon lafiya ya kamata gwamnati ta mayar da hankali ga wadannan abubuwa 4:

1. Mace-macen yara a lokacin haihuwa

Gididdiga game da yawan mace-macen yaran Najeriya wadanda suka mutu a lokacin haihuwa ba wani batun bane. Akwai misalai da yawa a asibitocin mu a wurare daban-daban kan kiwon lafiya a fadin kasar.

2. Zazzabin cizon sauro

Samar da gidan sauro mai magani bai isa ba. Dole ne a dauki matakan domin magance zazzabin cizon sauro a yankunan mu.

3. Tamowa

Yaran wanda ba a ciyar dasu da kyau daga haihuwar ba zasu fuskanci kalubale da dama a rayuwa. Kamar yadda ya ke fama da yunwa, za ya kuma fama da rayuwar ilimi.

KU KARANTA: IKON ALLAH! Wata mata mai shekaru 72 ta haihu a wannan jihar ta Arewa

4. Kyanda

Abin bakin ciki ne cewar yadda cutar kyanda ke kashe mutane musamman a arewacin Najeriya. Ya kamata gwamnati ta dauki kyakyawar mataki domin ta cece rayuwar yara talakawan Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon inda wasu yara ke rokon gwamnatin jihar Legas kada ta rushe gidajensu

Asali: Legit.ng

Online view pixel