An kama tantabarar dake safarar miyagun ƙwayoyi

An kama tantabarar dake safarar miyagun ƙwayoyi

- Abin mamaki, tantabara da safarar hodar Iblis

- Jami'an kwastam sun kama wata tantabara dauke da hodar iblis

Wani rahoto na jaridar Al-Rai dake kasar Kuwait ya bayyana cewar jami'an hukumar hana fasa kauri na kasar Kuwaita, kwatankwacin hukumar kwastam din Najeriya sun kama wata tantabara dake dauke da muggan ƙwayoyi a duburanta a hanyar ta shiga kasar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar an samu ƙwayoyin da yawansu ya kai 178 a cikin wani dan alaku da aka daure a duburan tantabarar.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta ƙaddamar da sabon sansanin dakarun sojojin ƙasa a Kafanchan

Wannan tantabara ta shiga hannu ne a lokacin data dira don ta huta a kusa da wani ofishin hukumar ta kwastam da ke garin Abdali kan iyakar Iraki kasar Iraki da Kuwait, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

An kama tantabarar dake safarar miyagun ƙwayoyi
Miyagun ƙwayoyin cikin jakar

Kaakakin hukumar, Abdullah Fahmi ya shaida cewa, jami'an kwastam sun dade suna da masaniyar cewa ana amfani da tantabaru wajen shigar da kwayoyi Kuwait, amma wannan ne karo na farko da suka samu nasarar kama tsuntsuwa.

Ko a shekarar 2015 sai da wasu masu gadi a wani gidan yari dake kasar Costa Rica suka kama wata tantabara dauke da hodar iblis da tabar wiwi a cikin wata 'yar jaka da aka daura mata.

An kama tantabarar dake safarar miyagun ƙwayoyi
Tantabarar

hakazalika shekarar 2011 Yansandan kasar Clumbia sun gano wata tantabara da ta kasa tashi wajen tsallake wani kurkuku mai tsayin gini, saboda nauyin da ya yi mata yawa na hodar iblis da nau'o'in tabar wiwi da aka daura mata dako.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jam'iyyar APC yaya dai?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng