IKON ALLAH! Wata mata mai shekaru 72 ta haihu a wannan jihar ta Arewa
- Wata mata mai suna Misis Magdalene Francis 'yar asalin Jihar Filato ta samu cimma babban burin ta na rayuwa, wanda bai wuce samun haihuwa ba, bayan tsawon shekaru da ta yi tana nema ita da mijinta Mista Francis Davou.
- Ita dai wannan mata wacce ta yi ritaya daga aiki bayan ta cika shekaru 60 a duniya, inda ta yi amfani da kudaden da ta samu na sallama daga aiki ta shiga neman mafita ga bukatar ta, ta hanyar amfani da fasahar kimiyya.
Legit.ng ta samu daga majiyar mu ta Zuma Times cewa Madam Magdalene ta nemi a yi mata dashen ciki a wani asibiti mai zaman kansa da ke Jos, wanda ya kware kan wannan aiki, inda aka yi mata gwaje gwaje ita da maigidanta, kuma har aka gudanar da aikin da ake bukata. Sai dai aikin da aka yi ba a dace ba, kamar yadda likitocin suka bayyana, ba kowanne lokaci ake dacewa ba.
Amma duk da haka wannan iyali ba su fitar da tsammani ba, domin kuwa bayan nacin addu'o'i da gwaje gwaji, an sake jaraba aikin har sau hudu, inda aka yi dace daga bisani cikin ya zauna, har kuma aka yi mata aiki aka ciro jaririyarta. Tubarkallah!
Yanzu haka dai wadannan ma'aurata na nan cikin godiyar Allah da farin cikin amsa addu'ar su da Ubangiji ya yi, bayan shekaru 39 suna nema.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng