"Lalle Buratai ne ya ceci Najeriya daga juyin Mulki" - inji Aregbesola, Gwamnan Osun
- An ruwaito jita-jitar wasu nason su hambaras da dimokuradiyya
- An sami sunayen masu wannan kokarin
- Sojoji sun ce sun gano bakin zaren
A makonnin nan da suka shude, anji yadda ake ta yamadidi da batun wai wasu yan siyasa na jawo soji a jika da kiran su watsar da gwamnatin Buhari, kamar dai yadda aka taba yi masa a baya.
Ba'a san suwaye ba domin hukumomi sun ki fadin ko su waye. An dai kula da bizi-bodi da manyan kasarnan suka rinka yi a daga Abeokuta zuwa Minna, zuwa Abuja, zuwa Maiduguri, har ma da wasu na kira da shugaban yayi murabus, wasu kuma na cewa bai bar kowa a kan karagar iko ba.
KU KARANTA KUMA: "Ba wasu 'yan matan Chibok da aka sace, duk wasan kwaikwayo ne" - Inji Labour Party
Shekaru biyu kenan da aka fara mulkin jam'iyyar Adawa, siyasa kuma ta fara zafi domin gabatowar zabuka masu zuwa. An dai jiyo babban hafsan soji na kasa na tsawatarwa da soji da kada su kuskura su tsoma baki a harkar mulki ko siyasa, su tsaya a iya aikinsu.
Gwamnan Osun Rauf Aregbesola ya nanata cewa Buratai dinne kawai yayi kokarin katabus ya dakile mugun nufin na masu son juyin mulki.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng