An damke mutum 141 a liyafar 'yan luwadi a kasar da tafi yawan Musulami a duniya

An damke mutum 141 a liyafar 'yan luwadi a kasar da tafi yawan Musulami a duniya

Hukumar 'Yan sandan kasar Indonesiya ta yi ram da mutane 141 wadanda suka halarci wata liyafa ta 'walimar 'yan luwadi,' a Jakarta, babban birnin Indonisiya ranar Lahadi.

'Yan sanda sun ce wadanda suka halarci liyafar sun hada da wani dan BIrtaniya da dan Indonesiya, sun kuma biya dala 10 don su halarci liyafar.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar matsin lamba ga 'yan madigo da luwadi duk da cewan basuda yawa yanzu a kasan.

Duk da yawan mabiya addinin Islaman da ke kasan , dokar Indonesiya dai ba ta haramta luwadi ba, sai a yankin Aceh kawai.

KU KARANTA: Obasanjo ya kai ziyara jihar Borno

Amma mai magana da yawun 'yan sandan Jakarta Raden Argo Yuwono, ya ce za a tuhumi wasu daga cikin mutanen da aka kama din a karkashin dokar hana Batsa.

Ya shaida wa BBC cewa, "Akwai 'yan luwadin da aka kama su tsirara suna kuma tattaba jikinsu da nufin jin dadi."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng