Manoma a Gombe sun yi babban girbe, tan dubu 9,000 na alkama
- Manoma a jihar Gombe sun yi babbar girba, kowa na darawa
- Noman alkama ana yinsa ne da sanyi
- Sayar da kayan gonar baya wa manoman wahala muddin sun ciro daga gona
A bana, maoma na darawa, bayan da suka girbe alkama har tan 9,000 a jihar Gombe, a noman 2016/2017, hakan na zuwa ne ta bakin Batari Dauda, shugaban kungiyar manoma ta jihar, a hirarsa da manema labarai.
Yace dukda cewa burin su na tan 10,000 ne, wannan labarin darawa ne. Ya ta'allaka gazawar hakan kan irin iri da suka samu da vkuma karancin kayan aiki na noma, dama karancin shi kansa irin, hade da makarar wasu manoman dab da shuka.
Ya bada bayanin cewa, noman alkama anayin sa ne da sanyi ba da damina ba, duk wanda ya wuce watan Nuwamba bai fara dashe ba to kuwa bazai ga da kyau ba. HAka ma dai watan girbe shine watan Maris, ba'a so a wuce hakan.
A bangaren sayarwa kuma, yace sun sami zama gemu-da-gemu da manyan kamfanuwa masu bukatar alkamar, kuma sun ma ce bata ma ishe su ba. Ya kuma rufe da cewa, wasu tun kafin ka bar suto ma zasu saye a gida, don yin burodi da wain da sauran abinci na gab-da-gab.
Asali: Legit.ng