Wani babban hamshakin dan kasuwa ya bada tallafi sama da naira milyan 10 ga matasa a jihar Jigawa (Hotuna)

Wani babban hamshakin dan kasuwa ya bada tallafi sama da naira milyan 10 ga matasa a jihar Jigawa (Hotuna)

- Wani Babban hamshakin dan kasuwa ya tallafa wa mata da matasan jihar Jigawa da tallafinsa ta kai naira miliyan 10

- Dan kasuwar ya raba wa matasan sabbin babura, ya kuma rabawa mata kimanin su 150 jari kyauta

- M.Y ya tabbatar da cewa Insha Allahu nan da wata biyu zai sake gabatar da irin wannan tallafin ga ‘yan jihar Jigawa

Babban Hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Mukhtar kuma shugaban kamfanin Oil Nig Limited, ya yi wa mata da matasan jihar Jigawa tallafi a ranar Asabar, 20 ga watan Mayu. Inda ya raba wa matasan sabbin babura, wanda hawansa sai dan gata ga matasa har guda 20, ya kuma rabawa mata kimanin su 150 jari kyauta.

Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin Rariya kayayyakin sun hada da bada tallafin jarin kudi 10,000 ga mata guda 500 da bada tallafin babura kirar Bajaj guda 20 ga matasa su 20, wanda kudinsu ya kai 250,000 ga kowanne daya.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da alherin ya bayyana cewa babu shakka irin wannan yunkurin kalubale ne ga zababbun 'yan siyasa.

Wani babban hamshakin dan kasuwa ya bada tallafi sama da naira milyan 10 ga matasa a jihar Jigawa (Hotuna)
Sabbin baburan da aka rabawa wasu matasa a jihar Jigawa

Ya ce: "Idan har mutumin da ba takara ya yi ba, ba kuma zabar sa aka yi ba, amma yana yunkurin baiwa mata da matasa ruwan dimokaradiya su kurba, to ina ga kai da aka jefawa kuri'a ya kenan?"

Wani babban hamshakin dan kasuwa ya bada tallafi sama da naira milyan 10 ga matasa a jihar Jigawa (Hotuna)
Lokacin bada tallafin jarin kudi 10,000 ga mata guda 500

"Don haka muna kira ga sauran jagororin mu a tafiyar siyasar gidan Sardauna, da su yi koyi da wannan bawan Allah. Idan ana kamawa gwamna ta nan da can, sai ka ga alkhairin ya kai ga kowa", inji wanda ya ci moriyar kyautar.

Wani babban hamshakin dan kasuwa ya bada tallafi sama da naira milyan 10 ga matasa a jihar Jigawa (Hotuna)
Tallafin jarin kudi 10,000 ga mata guda 500

A Jawabinsa wajan taron M.Y ya tabbatar da cewa annnan shine karo na farko, Insha Allahu nan da wata biyu zai sake gabatar da irin wannan. Da sannu sai ya zaga ko'ina a jihar Jigawa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Kano Ganduje na ci gaba da ciwa Kwankwaso dunduniya

Wani babban hamshakin dan kasuwa ya bada tallafi sama da naira milyan 10 ga matasa a jihar Jigawa (Hotuna)
Babban hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Mukhtar kuma shugaban kamfanin Oil Nig. Limited a lokacin da yake bayani a wajen taron

Daga karshe ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su tallafawa matasa da arzikin da Allah ya hore musu don ganin an samu ci gaba a jihar Jigawa da kasar baki daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng