Khadija na bukatar taimakon ‘yan Najeriya da gaggawa (Hotuna)
- Ana neman kimanin naira milyan 5 don a yi wa wata yarinya mai shekaru 3 wanda take fama da ciwon zuciya aiki
- Ana neman taimakon ‘yan Najeriya da a tallafa wa yarinyan
- Likitoci a jihar Kano sun ce sai dai a kai ta kasar Indiya kafin a yi mata aiki
Wannan yarinya mai suna Khadija Ahmad tana fama da ciwon zuciya. Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin Rariya, likitoci sun nace sai an kai ta kasar Indiya kafin a yi mata aiki.
Khadija wadda take a yankin Sumaila Mandawri dake jihar Kano, likitoci sun bayyana cewa ana neman kimanin naira milyan 5 kafin a yi mata aikin.
Don haka ake bukatar taimakon al'umma daga ciki da wajen kasar nan, domin ganin an ceto rayuwar Khadija wadda ba ta wuci shekara 3 ba.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Kano Ganduje na ci gaba da ciwa Kwankwaso dunduniya
Ga masu bukatar tallafawa Khadija, za ku iya amfani da wannan Account Lamba:
ACC NO: 0002328275
NAME: Ahmad Muhammad Sumaila
BANK: Stanbic IBTC
Don karin bayani kuma za a iya kiran lambar wayar mahaifinta; 08036311515
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kali bidiyon wasu yara da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram
Asali: Legit.ng