Yarinyar marigayi Umaru Musa Yar’adua ta bada mamaki a waɗannan hotunan
- An watsa wasu kyawawan hotunan yarinyar marigayi Umaru Musa Yar'adua
- Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya mulki Najeriya ne daga shekarar 2007 zuwa 2010
A ranar 10 ga watan Mayu ke tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya riga mu gidan gaskiya, kuma tun wannan lokaci ba’a sake jin duriyar iyalinsa ba, har sai ranar Laraba 17 ga watan Mayu.
A ranar Larabar data gabata ne dai yarinyar sa, Aisha, ta fito da tsananin kyawunta sanye da wasu bakaken kaya, bayan ta sha fente fente daban daban irin na ado da kwalliya.
KU KARANTA: Bincken Sarkin Kano: Anyi cacar baki tsakanin majalisar dokokin Kano da majalisar wakilai
Wadannan hotunan Aishan sun fito ne daga shafin sadarwa na Instagram mallakin wata kwararriyar mai yi ma mata kwalliya da ado, wanda tayi ma Aisha nata kwalliyar.
Ga hoton nan:
Kwararriyar yar kwalliyar tayi ma hotunan Aisha taken “Barkan ku da safiya, ga fa Aisha nan ta fito cikin sabon kwalliya, minti 15 kacal aka dauka wajen yin wannan kwalliyar, ko a jiya da kwalliyar mu ta dinga yawo, da daren nan kuma da tazo, aiki kadan muka kara yi mata, sai ga shi ta fito a kyakkyawar ta.”
A wani labarin da Legit.ng ta samo, Aisha ta taba kin amincewa da tayin aure da attajirin nan Dangote yayi mata shekaru da dama da suka wuce, amma ana ganin hakan baya rasa nasaba da wani wulakanci da Dangote ya taba yi ma mahaifinta a lokacin zabukan 2007.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda wata mata tayi asarar yaronta
Asali: Legit.ng