Kasar Qatar ta kere sa’a, ta gina filin wasan ƙwallon ƙafa mai na’uran sanyaya ɗaki

Kasar Qatar ta kere sa’a, ta gina filin wasan ƙwallon ƙafa mai na’uran sanyaya ɗaki

- Qatar ta sanar da kammala katafaren filin wasan kwallon kafa da za’ayi amfani dasu yayin gasar cin kofin duniya

- Qatar ta samar da wani na'uran fasahar zamani da zai sanyaya filin wasan, saboda zafi

Gwamnatin kasar Qatar ta sanar da kammala aikin ginin katafaren daya daga cikin filayen wasannin kwallon kafa da za’ayi amfani dasu yayin gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakwanci a shekarar 2022.

A cikin wannan filin kwallo, akwai wani fasahar zamani da aka yi amfani da shi wanda zai samar da ni’ima da walwala ga yan kwallon da masu kallo, duba da tsananin zafin rana da ake fama da shi a garin.

KU KARANTA: Bincken Sarkin Kano: Anyi cacar baki tsakanin majalisar dokokin Kano da majalisar wakilai

Yadda wannan na’ura ke aiki kuwa shine zata dinga fesa ruwan sanyi a sararin samaniyar filin wasan, ta yadda filin zai yi sanyi, sa’annan na’urar zata buso wani isa da zai sanyaya filin wasan, inji rahoton rediyo Faransa.

Kasar Qatar ta kere sa’a, ta gina filin wasan ƙwallon ƙafa mai na’uran sanyaya ɗaki
Filin wasan

Wannan fili mai suna Filin wasa na Khalifa, tsohon filin wasa ne da aka gina a shekarar 1976, kuma yana cin sama da yan kallo 40,000, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Kalubalen zafin yanayi na daya daga cikin kalubalen da Qatar ta fuskanta kafin ta samu damar daukar nauyin gasar cin kofin na Duniya.

Kasar Qatar ta kere sa’a, ta gina filin wasan ƙwallon ƙafa mai na’uran sanyaya ɗaki
Flin wasan

Za a bude wannan katafaren filin kwallo ne da wani babban wasa da za’a buga tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafar kasar, Al-Sadd inda tsohon dan wasan Barcelona Xavi Hernandez yake da kuma kungiyar Al-Rayyan.

Wasan shine wasan karshe na gasar cin kofin sarkin Qatar, babban gasar kwallon kafa na kasar kenan.

Sakataren kwamitin daukar nauyi gasar, Hassan Al Thawadi yace “Yadda muka kammala gina filin wasan a yanzu, shekaru 5 kafin gasar, ya nuna cewa da gaske muke na daukan nauyin gasar.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng