Gobara ta yi mummunar ta'asa a wata sabuwar kasuwa a Arewa

Gobara ta yi mummunar ta'asa a wata sabuwar kasuwa a Arewa

Da asubahin yau ne wata gobara ta tashi a babban kasuwar garin Kontagora dake Jihar Neja inda aka yi asarar dimbin dukiyoyi. Shaguna da dama ne suka kone kurmus.

Da asubahin yau ne wata gobara ta tashi a babban kasuwar garin Kontagora dake Jihar Neja inda aka yi asarar dimbin dukiyoyi. Shaguna da dama ne suka kone kurmus.

Jami'an 'yan banga dake gadin kasuwar ne suka ga shaguna na ci da wuta, inda nan take suka nemi agajin al'umma, bada bata lokaci ba jami'an hukumar kashe gobara suka iso wurin domin kashe wutar.

Gobara ta yi mummunar ta'asa a wata sabuwar kasuwa a Arewa
Gobara ta yi mummunar ta'asa a wata sabuwar kasuwa a Arewa

KU KARANTA: Akwai maganar hambarar da gwamnati fa - Tsohon minista

Kawo yanzu dai ba a gano musabbanin tashin gobarar ba, sai dai shugabannin kasuwar sun ce suna ci gaba da bincike domin gano silar tashin gobarar.

Legit.ng ta samu labarin cewa al'umma da dama ne suka isa kasuwar domin jajantawa wadanda suka yi asarar dukiyoyin su, hakazalika sun yi kira ga 'yan kasuwar da su saukaka farashin kayaiyakin su alfarmar wannan wata na azumi da za'a shiga.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng