Dandalin Kannywood: Masoya sun bukaci Rahma Sadau ta aje girman ka don a maido ta harkar fim
- Sanin kowa ne musamman masu bin fina-finan Hausa cewa Rahama Sadau na daya daga cikin wadanda tauraron su ke shanawa kafin a dakatar da Ita daga fagen shirya fina-finan Hausa.
- Bayan dakatar da Ita da akayi sanadiyyar fitowa a wata waka da tayi da mawakin nan mazaunin garin Jos mai suna Classiq abin sai ya zama mata kamar wata sabuwar daukaka ne domin bayan haka har kasar Amurka ta tafi.
Abin da yake ci wa mutane tuwo a kwarya shine har yanzu fa ita Rahama ba ta nemi sulhu da Kungiyar MOPPAN ba tun bayan dakatar da ita da kayi. Su kuma MOPPAN din basu ce komai ba kai har yanzu.
Hassana Dalhat, ta yi wa gidan jaridar Premium Times nazari akan hakan kuma ta gano cewa lallai mafi yawa daga cikin masu sha’awar wasan finafinan Hausa na kaunar jarumar kuma kusan duk wanda ta tattauna da shi ya na rokon jarumar da ta nemi wannan sulhu tsakaninta da kungiyar MOPPAN din.
Legit.ng ta samu labarin cewa Maryam Mohammed, wanda malamar makaranta ce a Kaduna, ta ce “ Rahama jarumar mu ce amma dai ta cika fushi ne da riko. It ace karama kuma abin da ake zarginta da yi ta aikata, sai ta saukar da kanta ta nemi sulhu da kungiyar MOPPAN din. Hakan bazai rage ta da komai ba amma kuma ko don masoyanta ay ta hakura tayi musu hakan.
“Idan har tayi hakan to, su kansu MOPPAN din zasu hakura su amince ta dawo fim.
Habiba Shuraihu da ga jihar Bauchi ta ce tun bayan dakatar da Rahama Sadau ta dai na kallon finafinan Hausa.
“Daga bayabayan nan ne na dawo kallon finafinan Hausa. Amma rashin Rahama Sadau ya na ci mini rai. Ina matukar kaunar wannan baiwar Allah. Mu na rokonta ta nemi sulhu akan abin. Mu na turancin nan bashi bane Hausa shine namu kidawo ki ci gaba da abinda kikeyi kawai.
Da yawa daga cikin wadanda suka zanta da Hassana Dalhat, sun tabbatar mata da cewa idan da za su sami damar ganin Rahama Ido da Ido da sun roke ta da ta nemi sulhu.
KU KARANTA: Anfanin tafarnuwa 7 a jikin dan adam
“Tunda laifi tayi aka hukuntata, sai ta nemi sulhu. It ace karama ba laifi bane ki koma ki yi nadama akan abinda kikayi sannan ki ci gaba da sana’arki wanda shine mu muke so mu ganki a ciki ba fim din da ba na mu ba.
“Wallahi duk wanda yake ce mika ki rabu da fim din Hausa ba masoyinki bane. Kuma kowa fa kansa yake yi wa abu. Ki hakura ki koma ki ci gaba da aikinki.
Akalla Mutane sama da 50 ne Hassana ta tattauna dasu akan rashin Rahama Sadau a farfajiyar Finafinai kuma sun nuna takaicinsu akan rashin dawowarta har yanzu farfajiyar.
Rahama dai yanzu ta koma shirya finafinai da yan kudu tun bayan koranta da akayi.
Hamza Awwal yace idan dai Rahama ta damu da mu masoyanta da kuma wadanda suke juyayin rashinta a fim za ta yi amfani da wannan bayanai na mu masoyanta ta dawo fim.
“Kije ki roke su ki dawo ko don mu masoyanki.”
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng