Gwamnan jihar Kogi ya kai karar dan jarida saboda ya kwarmata cewa an damfara sa
- Wani dan jarida mai suna Austin Okai ya shiga ragar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, sakamakon wani rubutu da ya yi a shafin sa na Facebook
- Dan jaridar dai ya rubuta cewa, wasu batagari sun damfari Gwamnan jihar wasu makudan kudade har naira biliyan biyu da miliyan biyu.
Wannan ce ta sa gwamnan ya umarci lauyoyinsa shigar da kara domin karyata rahoton da kuma hukunta dan jaridar wanda ake zargi da yada jita jitar batanci ga gwamnan.
Legit.ng ta samu labarin cewa shi dai Okai bayan kasancewar sa dan jarida har wa yau kuma shi ne shugaban wata kungiyar matasa dake goyon bayan jam'iyyar PDP a jihar. Don haka ne ma ake zargin bayan nan da ya rubuta ya yi ne domin bata sunan gwamnan kasancewar sa dan adawa.
KU KARANTA: Anfanin tafarnuwa 7 a jikin dan adam
A yayin zaman farko da babbar kotun tarayya dake Lokoja lauyan wanda ake kara ya yi korafin shigar da sunan gwamnatin tarayya cikin jerin masu kara, a maimakon gwamnatin jihar, tun da Gwamnan jihar ne yake da karar ba rundunar 'yan sanda ba.
Don haka an bukaci a yi gyara ga yadda aka gabatar da karar, sannan aka daga cigaba da karar har zuwa wani lokaci a karshen wannan wata.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng