Shin wanene Nnamdi Kanu? Kuma mecece kungiyar IPOB?
- Nnamdi Kanu dan kabilar Igbo ne mai fafutukar kafa kasar Biyafara a kudu maso gabashin Najeriya.
- An bashi sunaye da dama na karramawa a kasar Igbo.
- Kamar dai Ojukwu wanda yaso kafa Biafra, shima gwamnatin Najeria ta saka sunansa a matsayin mai cin amanar kasa.
An manta shaf da batun yakin basasa na Najeriya, wanda aka kwashe shekaru biyu da rabi ana yi, a shekarun 1967-1969, wanda Janar Ojukwu ya jagoranta, kwatsam, sai wasu 'yan ta-kife a kasashen Turai, suka kafa rediyo, suna watsawa a tashoshin yanar gizo, domin jama'ar Ibon Najeriya, su kafa tasu kasar.
Musamman ma dai ganin yadda Janar Buhari ya ci zabe, wanda ya nuna a sau da yawa bai damu da su 'yan kanilar ba, wanda ya kuma fito daga yankin da ake ganin baya kawo arziki a hadakar najeriya.
Ya iso Najeriya a shekarar 2015, bayan hawan Shugaba Buhari, ya sauka a birnin Ikko, sai jami'an tsaro na DSS suka chafke shi a masaukin sa, suka kuma tsare shi ba tare da tuhuma ba, tsawon lokaci. An gurfanar dashi a kotu, an tuhume shi da laifin tunzura jama'a, da cin amanar kasa, da ma ingiza jama'a su dauki makamai.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Adamawa da Kamfanin Mai na NNPC zasu hada kai don samar da Makamashin zamani
Ita kuma kungiyar IPOB tana nufin kungiyar 'yan asalin Biyafara, a turance, ana kuma iya alakanta kungiyar da MASSOB, da MEND a burinsu na samun 'yantacciyar kasa. A tsarinsu kuma, kasar najeria, auren dole ne turawan mulkin mallaka suka yi musu.
KU KARANTA KUMA: Uwargidar shugaba Buhari ta kaddamar da gina asibiti a Daura
Yanzu dai, a fahimtar masu sharhi, samun damar mulkar Najeriya, ga kabilar Ibo, shine kadai abu da siyasance zai bawa mutanen gabas na Najeriya fahimtar cewa ba ware su ake ba, ba kuma mulkin mallaka Fulani ke musu ba, kamar dai yadda suke yawan zargi, tun kafa Najeriya.
Ku neme mu a shafin mu na facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Ko na twitter https://twitter.com/naijcomhausa
Shin ya kamata shugaba Buhari ya mika wa mataimakin shugaban kasar Osinbajo mulki?
Asali: Legit.ng