Kotu ta yanke wa wasu ‘yan luwadi 2 hukuncin bulala 85
- Wata kotu a kasar Indonesia ta yanke wa wasu Indonesia biyu hukuncin bulala 85 a bainar jama’a don yin luwadi
- Mutanen biyu sun ce ba zasu daukaka kara a kan hukuncin ba
Wani kotun musulunci a kasar Indonesia a ranar Laraba, 17 ga watan Mayu ta yanke wa wasu maza biyu ‘yan kasar Indonesia hukuncin bulala 85 don yin luwadi.
Wani kwamitin alkalai ne suka yanke wannan hukuncin bulala wanda za a yi a idon jama’a kuma karon farko da za a gabatar da irin wannan hukunci kan yin luwadi tun da aka gabatar da dokan a shekara 2014.
Wannan jumla ya na da tsanani fiye da bulala 80 da mai gabatar da arraraki ya bukaci.
KU KARANTA KUMA: Albishirin ku masoya Buhari ga sako daga fadar shugaban kasa (Karanta)
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Alkalin kotun, Khairil Jamal, ya ce a cikin sanarwasa cwaa, wadanada ake tuhuma sun tabbatar da aikata luwadin da kuma amsa laifin.
Duk da haka, mutanen biyu sun wakilci kansu a kotu kuma sun ce ba zasu daukaka kara a kan hukuncin ba.
Za a yi wa mutanen bulala a lokacin da za a gudanar da wani biki a ranar 23 ga watan Mayu, a lardin birnin Banda Aceh, inda masu sintiri suka kama su.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce, kyamar luwadi na karuwa a kasar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus daga cocin Living Faith Church
Asali: Legit.ng