Wani dan gwagwarmaya zai fuskanci hukuncin kisa don yin ridda
- Wani dan fafutuka zai fuskanci hukuncin kisa don yin ridda daga addinin musulunci zuwa ga wayanda basu yarda da Allah ba
- Hukumar 'yan sandan kasar ta ce Mohamed Al-Dosogy nada tabuwar hankali don haka ba za a iya hukuntashi kan zargin ba
Mista Mohamed Al-Dosogy, wani dan fafutuka wanda ke kokarin yin ridda zuwa ga wayanda basu yarda da Allah ba. Wannan mutumin dai ya shiga baban matsala a kasar Sudan inda hukumomi suka umarnin da a kama shi kan kaucewa Allah kuma wannan laifi nada hukuncin kisa a shari’ar kasar.
A cikin dokar shari’ar kasar Sudan ridda na matsayin babban laifi kuma duk wanda aka samu da laifin yin ridda zai fuskanci hukuncin kisa.
A ranar Litinin, 8 ga watan Mayu ne 'yan sanda a birnin Khartoum suka kama Al-dosogy kwanaki biyu bayan da ya nema damar mai shari’a don yin ridda daga addinin musulunci zuwa ga wayanda basu yarda da Allah ba.
![Wani dan gwagwarmaya zai fuskanci hukuncin kisa don yin ridda Wani dan gwagwarmaya zai fuskanci hukuncin kisa don yin ridda](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt3op1t5ddqrf.jpeg?v=1)
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, hukuma ‘yan sanda dai ta saki Al-Dosogy a ranar Juma'a, 12 ga watan Mayu kan umurnin mai shari’a.
KU KARANTA KUMA: Yan mata 3 sun kai harin ƙunar bakin wake a Borno, mutane 2 sun mutu
'Yan sanda sun ce Mohamed Al-Dosogy nada tabuwar hankali don haka ba za a iya hukuntashi kan zargin aikata wannan laifi ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus daga cocin Living Faith Church
Asali: Legit.ng