JAMB ta saki sakamakon jarrabawa

JAMB ta saki sakamakon jarrabawa

- Hukumar JAMB ta fito da sakamakon jarrabawar UTME da aka gudanar a ranar Asabar

- Rajistara na hukumar da karamin ministan Ilimi sun ziyarci wasu wuraren jarrabawar a Kogo da ke Bwari

Hukumar JAMB ta fito da sakamakon jarrabawar UTME da a gudanar a ranar Asabar, 13 ga watan Mayu.

Rajistara na hukumar, Farfesa Is-Haq Oloyede ya tabbatar da wannan labari ne yayin da yake magana a lokacin ziyarar saka idanu ga wanda suke rubuta jarrabawar UTME tare da karamin ministan Ilimi, Farfesa Anthony Anwukah a Abuja.

Oloyede da Anwukah sun ziyarci wuraren jarrabawar Digital Bridge Institute, Global Learning Institute, Sascon International School da kuma JAMB CBT Center a Kogo, Bwari.

JAMB ta saki sakamakon jarrabawa
Masu jarrabawar UTME

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya sha ruwan addu’o’i a Jihar Legas

Legit.ng ta ruwaito cewa Oloyede ya nuna gamsuwa kan yadda ake gudanar da jarrabawar yanzu, kuma ya ce kokarin 'yan takaran babu laifi.

Rajistara na hukumar ya ce: "Sakamakon jarrabawar UTME ya fito da kuma kokarin 'yan takaran babu laifi. Amma muna tabbatar da cewa wannan shi ne sakamakon yanzu maimakon tunanin za a iya samun sakamakon ta wani hanya. "

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Femi Fani Kayode ya bayyana cikakken bayani kan maganarsa da shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel