Hauka ko Talauci? Wata mata ta saida yar cikinta a N250,000

Hauka ko Talauci? Wata mata ta saida yar cikinta a N250,000

- Wata budurwa ‘yar shekara 22 tare da wasu mutane shida da ake zargi da dillacin sai da kananan yara sun shiga hannun jami;an tsaro.

- Ita dai wannan mata sunanta Onyinyechi Osoneye anyi nasarar kama ta a ranar labara ta hanyar taimakon wani jami;in sirri dake bincike akan irin wannan ta’addanci.

Osoneye ta shaidawa manema labarai cewa ta saida diyar ta ne ga wani mutum maisuna Mr Ike Nwata dake zaune a garin legas.

Legit.ng ta samu labarin cewa yanzu haka jami’an tsaro sun garzaya zuwa gidan su wannan mata maisuna Osoneye domin jin ta bakin mahaifiyarta,Mahaifiyar Osoneye ta shaidawa jami’an tsaro cewa wannan abu ya faru ne a dalilin wani saurayin Osoneye da yayi mata ciki,sannan kuma bayan an neme sa akan batun cikin sai ya nuna kamar bai san da labarin cikin ba.

Hauka ko Talauci? Wata mata ta saida yar cikinta a N250,000
Hauka ko Talauci? Wata mata ta saida yar cikinta a N250,000

KU KARANTA: Yadda nayi shigar maza don in samu aikin yi

A karshe dai anyi ram da Osoneye Mahaifiyar karamar yarinyar tare da mutane shida data saidawa diyar ta akan kudi naira N250,0000,Inda yanzu an mika wannan yarinya zuwa gwamnatin jihar legas dake hedikwatar Ikeja domin a kara zurfafa bincike.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel