Yan sara-suka su 11 sun gamu da fushin wata kotu a jihar Bauchi

Yan sara-suka su 11 sun gamu da fushin wata kotu a jihar Bauchi

- Babbar kotun majistri ta jihar Bauchi ta aika da yan sara suka gidan yari

- Jami'an hukumar yansanda ne suka kama su a yayin da Yakubu Dogara ke kaddamar da aikace aikace

Wata kotun majistri ta aika da yan Sara-suka dake harkar barandan siyasa su goma sha daya zuwa gidan yari a jihar Bauchi bayan ta kama su da laifuka daban daban.

Kaakakin yansandan jihar Bauchi, SP Haruna Mohammed ya bayyana cewar a ranar 6 ga watan Mayu ne jami’an yansanda suka kama yan sara suka 11 a lokacin da Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya kai ziyarar aiki jihar Bauchi.

KU KARANTA: Sojoji sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kama 1 a dazukan Bauchi

Bayan kammala bincike ne sai hukumar yansandan ta gurfanar dasu gaban babban kotun majistri dake garin Bauchi a ranar 9 ga watan Mayu, inji rahoton Daily Trust.

“Ana tuhumar mutane 9 daga cikinsu da aikata bangan siyasa da kuma hada kai wajen aikatawa haka, kuma sun amsa laifukansu, hakan ya sanya alkali yanke musu hukuncin daurin shekara 1 a gidan yari, ko su biya taran N53,000.” Inji Kaakakin yansanda.

Yan sara-suka su 11 sun gamu da fushin wata kotu a jihar Bauchi
Yan sara-suka

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sanarwar ta cigaba da fadin “Sauran guda 2 kuma sun amsa laifukan da ake tuhumarsu akai, suma an yanke musu watanni 19 a gidan yari.”

Daga karshe sanarwar ta umarci kowanne daga cikin wadanda aka yanke ma hukuncin da ya biya N15,000 ga mutanen da suka ji ma ciwo da wadanda suka afka ma wa, idan ba haka ba kuma su fuskanci zaman gidan yari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda yan Sara suka suka hallaka wani yaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng