Hauka! Bakin kishi yasa wata mata ta datsewa kishiyar ta hannu

Hauka! Bakin kishi yasa wata mata ta datsewa kishiyar ta hannu

Jama'a ku dubi wannan baiwar Allah mai suna Halima Ayuba 'yar asalin kabilar Gwari wanda wani ya aureta ya kai ta Zaria a matsayin matar sa ta biyu, kuma ta zamanto mai kulawa da shi fiye da matar sa ta farko, don haka ta kwallafa kishinta a rai har ya kai ga ta dauki adda mai kaifi ta sare mata hannu.

Legit.ng ta samu labarin daga Zuma Times cewa yanzu haka wadda ta yi wannan danyen aiki mai suna Laraba Muntari tana hannun hukuma, kuma za su mika ta kotu nan bada dadewa ba.

A wani labarin kuma, wata kotu dake Ikejan Jihar Legas ta tuhumi wani mutum mai suna Folorunsho Oluwaseun, da laifin yiwa yarsa mai shekaru goma 17 Fyade.

Hauka! Bakin kishi yasa wata mata ta datsewa kishiyar ta hannu
Hauka! Bakin kishi yasa wata mata ta datsewa kishiyar ta hannu

Kotun ta bada belin Mista Oluwaseun kan kudi naira 300,000 da kuma mutane biyu daza su tsaya masa.

Mutumin da yake zaune Ofin dake Ikorodun jihar Legas ,yana fuskantar tuhumar laifin aikata fyade.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng