'Yan bindiga sun kashe mutane 21 a wani harin da suka kai a masallaci a jihar Nijer

'Yan bindiga sun kashe mutane 21 a wani harin da suka kai a masallaci a jihar Nijer

Wasu mahara da ba a san ko suwaye ba sun kai wani hari a cikin masallacin kauyen Etogi dake cikin mazabar Gbara ta karamar hukumar Mokwa dake jihar Niger, inda suka kashe masallata 21 a lokacin sallar asubar ranar Lahadi ciki har da limamin masallacin.

Majiyar mu ta The Nation ta rawaito cewa kai harin bai rasa nasaba da wata hatsaniya da nutanen kauyen suka yi da wasu matasan Fulani a yankin nasu wanda ya sanadiyyar mutuwar dan Fulani daya a lokacin.

'Yan bindiga sun kashe mutane 21 a wani harin da suka kai a masallaci a jihar Nijer
'Yan bindiga sun kashe mutane 21 a wani harin da suka kai a masallaci a jihar Nijer

KU KARANTA: Ba mamaki karshen Babachir ya zo

Legit.ng ta samu labarin cewa majiyar ta bayyana cewa rashin jituwar ta shiga ne sakamakon jajircewa da matasan garin suka yi na cewa Fulanin sai sun biya kudin wani fili da suke zaune domin na mai garin garin ne, inda su kuma Fulanin suka yi ikirarin cewa wajen nasu ne.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar Yan sanda jihar DSP Bala Elkana ya bayyana cewa mutane 20 suka mutu inda 8 da suka sami manyan raunuka aka wuce da su zuwa asibiti.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng