A shekara 16 nayi ciki kuma na zama miliyoniya a shekara 17, inji shahararriyar ‘yar wasan Nollywood

A shekara 16 nayi ciki kuma na zama miliyoniya a shekara 17, inji shahararriyar ‘yar wasan Nollywood

Kyakyawar yar wasan Najeriya da kuma tauraruwar dake haska fina finai a shekarun baya ta bayyana sirrin ta a filin wanda da yawan jama’a basu sani ba.

Hilda Dokubo ta bayyana sirrin da ya baiwa jama’ar mamaki kan irin rayuwa da ta fuskanta a shekarun baya, Jarumar dai ta kasance yar asalin jihar Ribas a yankin kudu maso kudancin kasar da tauraronta ya dade yana haskawa a fina finan Nollywood tun a zamanin da, inda daga bisani ta afka siyasa tana zaman mai baiwa tsohon gwamnan jihar Peter Odili shawara kan harkokin da ta shafi matasa.

A lokacin da Hilda ke bayyana tarihin ta ga duniya, ta nuna irin juyin rayuwa da ta fuskanta inda take cewa:

“A da babu abin da muka rasa na jindadin rayuwa a duniya amma saboda kaddara irin na mutuwa yasa muka zama abin tausayi a rayuwa.

KU KARANTA: Jihar Adamawa ta kafa dokar yiwa masu shirin aure gwajin kwayar kanjamau

“A lokacin da babana ya rasu mun fuskanci kunci rayuwa irin na talauci inda hakan ya haifar wa mamana da cutar ciwon kwakwalwa.

A shekara 16 nayi ciki kuma na zama miliyoniya a shekara 17, inji shahararriyar ‘yar wasan Nollywood
Hilda Dokubo

“Kaiwa da kawowan harkokin yau da gobe na hadu da wani mutum da ya bani kwangilar ma’ajiyar mai na miliyan 2 abin da ya bani matukar mamaki saboda tun da nake a rayuwana ban taba rike kudin da yayi sama da dubu 100 ba, sai na fara ganin kaina a matsayin hamshakiyar mai kudi a shekara 17.

“Na kasa samun kyakyawan sakewa da hutawa ganin yawan adadin wannan kudin, amma samun wannan ba zai hana ka afka cikin abinda Allah ya kaddara maka ba.”

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yan wasan da waka

Asali: Legit.ng

Online view pixel