Ra'ayi: Karya fure take bata 'ya'ya - Daga Farfesa Salisu

Ra'ayi: Karya fure take bata 'ya'ya - Daga Farfesa Salisu

Labari ya baza duniya cewa bikin 'yar gidan wa'e ya samu halartar manyan kurayen kasa. Wai an ga cincirindon jiragen sama na kashin kai (ba mallakar gwamnati ba) wajen guda talatin (30)!

Da ma Hausawa Sun ce a bikin farar kaza, ba sai an gayyaci balbela ba. Ashe kuwa idan babbar kura za ta yi biki, Ai dole kananan kuraye su hallara.

To amma, wannan irin bayyana ta alfahari da baje kolin jiragen da duk kowa ya san da dukiyoyin babakere aka sayesu me yake nunawa? Shin wadannan kurayen suna nunawa talakwa cewa basu daddara ba ne?

Dadin abin dai shi ne ita karya fure take bata 'ya'ya. Duk wannan cincirindon jiragen saman ta gina ne bata shiga ba. Ita babbar kura ta yi mulki na shekaru takwas amma bata shiga zukatan talakawa ba. Shi kuwa mai talakawa, shekara biyu kacal ya yi yana mulkin amma Allah Ya wanzar da kaunarsa a zukatan talakawa har tsawon shekaru talatin basu daina kaunarsa ba. Shi kuma gashi bashi da jirgin babakere da wawura ba. Allah ne da talakawa suke tare da shi, amma duk da haka basu daddara ba?:Tabdi jam, "walau ja'at hum kullu aayatin hatta yarau al-azhabal 'aleem"'.

Hmmm, me jiya ma ta yi ballantana yau!

Allah karawa PMB lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel