Abincin wani-gubar wani: Kasuwar Kwadi na cigaba da bunkasa a arewa

Abincin wani-gubar wani: Kasuwar Kwadi na cigaba da bunkasa a arewa

Yanzu haka dai a Najeriya sana'ar kamawa da sayar da kwadi wadanda ake ci kamar kifi na kara bunkasa, a wasu sassan arewacin kasar, wanda wannan abu ne da wasu ke kyama ganin kamar ya saba wa al'adarsu.

Daya daga cikin irin garuruwan da wannan sana'a yanzu ke bunkasa shi ne garin Chiromawa a jihar Kano da kuma Hadejia a jihar Jigawa, inda za ka ga 'yan kasuwa yawanci 'yan yankin kudu maso gabashin kasar da kuma jihar Benue da ke yankin arewa maso tsakiyar kasar na cuncurundo a kasuwannin da ake wannan hada-hada.

Legit.ng ta samu labarin cewa Sakataren dillalan kwadin a kasuwar ta Hadejia Aliyu Isama'il Mala, ya shaidawa BBC cewa, su kam wannan kasuwancin na su sai hamdala, duk da kallon ban bara kwan da wasu ke musu kan sana'ar.

Masu wannan sana'a dai na korafin a kan rashin ware musu wuri mai kyau da zasu gudanar da wannan sana'a ta cinikin kwadi.

Abincin wani-gubar wani: Kasuwar Kwadi na cigaba da bunkasa a arewa
Abincin wani-gubar wani: Kasuwar Kwadi na cigaba da bunkasa a arewa

KU KARANTA: Real Madrid ta samu nasar kaiwa wasan karshe na kofin zakarun Turai

Ba dai duka nau'in kwadin ake sayar da su fa, misali nau'in kwado na tudu, ba a cin sa, saboda ya na da dafi, dan haka ba a sayar dashi.

Sauran kwadin da ba a kama su har ta kai da anyi bandarsu an sayar sun hadar da, Kurnu da Dan sanda da Bididdigi.

Yanzu dai kasuwancin kwadi na bunkasa, ganin yadda masunta da ma kabilu da dama ke shiga cikinsa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng