Za ayi bikin ɗiyar IBB, Halima, da angonta Sarkin Sudan Gombe

Za ayi bikin ɗiyar IBB, Halima, da angonta Sarkin Sudan Gombe

- Tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida zai aurar da yarsa Halima a ranar Juma'a

- Halima Ibrahim Badamasi Babangida zata auri angonta Alhaji Auwal

Yarinyar tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Halima zata angwance da mijinta Alhaji Auwal Lawal Abdullahi a ranar Juma’a 12 ga watan Maris a garin Minna.

Halima itace ya ta karshe ga marigayya matar IBB, Maryam Babangida, shi kuwa mijin nata, Alhaji Auwal Dan kasuwa ne kuma yana rike da sarautar Sarkin Sudan Gombe.

KU KARANTA: Anyi aringizon kasafin kuɗin bana da naira miliyan dubu 149 a majalisa

A cikin shirye shiryen bikin, hukumar yansandan Najeriya tayi alkawarin habbaka tsaro a gidan IBB da kewayensa, inda tace zata jibge jami’an yansandan 4000 akan manyan hanyoyin jihar Minna, fili sauka da tashin jirage da kuma gidan bikin.

Za ayi bikin ɗiyar IBB, Halima, da angonta Sarkin Sudan Gombe
Amarya Halima

Haka zalika, Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar jami’an tsaron farin kaya, NSCDC yace zasu aika da jami’an su 135 domin tabbatar da tsaro a yayin bikin da bayan bikin.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito za’a daura auren ne da misalin karfe 2:30 na ranar Juma’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayin Yan Najeriya dangane da tafiyar shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng