Sakin yan matan Chibok abin farin ciki ne - Gwamnatin Amurka

Sakin yan matan Chibok abin farin ciki ne - Gwamnatin Amurka

- Sakin yan matan chibok guda 82 daga hannun matsara yan Boko Haram bayan shekaru uku abin farin ciki ne a cewar gwamnatin Amurka

- Mr Nathan Holt tabbatar da cewa Najeriya kawar Amurka ce ta kut da kut a mafiya yawancin ayyukansu da sukeyi a gurare da majalisar dinkin duniya

Mr Nathan Holt, mataimakin Darakta a ofishinsu na yammacin Afirka karkashin Afurka ne yayi wannan jawabin a Washington DC a wani taro yayinda ya nuna Najeriya kawa ce ta kut da kut ga gwamnatin kasar tasu.

Mafi yawancinku sun bibici labaran sakin yan matan a satin da ya gabata, kuma a zahiri hakan na tabbatarda farin ciki wa su yan matan da yan'uwansu da suka dade basu gani ba.

Mr Holt ya kara da cewa, “a kwai bukatar muyi tsokaci kan cewa su din kadan ne daga tarin mutanen da yan Boko Haram da takwarorinsu; wato ISIS a yammacin Afurka suka kame."

Dan Amurkan ya tabbatar a rahoton Legit.ng cewa gwamnatinn Amurka tana nan tana kara tabbatarda ayyukan hadin guiwa da Najeriya da UN gun tabbatar da abubuwan da suka dace wa tsari mai kyau saboda kasantuwar Najeriyan uwa mai tacewa a yankin kasa na Afurka.

Ya kara tabbatar da cewa najeriya abokiyar aikin Amurka ce a mafiya yawancin ayyukansu da sukeyi a majalisar dinkin duniya.

KU KARANTA: Daya daga yan Matan Chibok da taki dawowa cckin farinci nake tare da mijina a inda nake

Daga ayyukan da mukayi tare akwai misalin mas'alar makaman Nukiliya da sauransu.

Holt ya nuna rashin jindadi da sukayi na fadawar yaran hannun yan ta'addan a karon farko da hakan ya haifar da rshin nutsuwa ma gwamnatin kasa baki daya.

ya nuna cewa suna cikin farinciki gameda jama'a dake samun damar komawa mazaunansu bayan aukuwar tashin-tashinar da rikicin ya haifar tun daga shekarar 2009 kawowar yau.

jajircewa sojoji da jami'an tsaro kadai bazai wadatu ba ba tareda taimakon yan Najeriya daidaiku ba. Muna nan muma muna kuma zamu ci gaba da bada taimakon mu wa mutanen da hakan ya auku dasu da karfafar jami'an tsaro.

A karshe, ina ganin mu da kawarmu Najeriya zamu fahimci cewa kawo karshen wannan yakin ba na mutum daya kadai bane, akwai bukatar cinma manufar bukatun mutane na ilimi,tacarcen ruwan sha da sauransu a yankunan rikicin."

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel