Ayi taka tsan-tsan: Zakuna 5 sun tsere, sun shiga gari
-Wasu muggan zakuna guda 5 masu tsananin mugunta sun tsere daga gandun dabbobi
-An gargadi jama'a dasu bi a hankali, kuma su kula da hanyoyin da suke bi
Hukumar gandun namun daji ta Afirka ta kudu ta yi kira ga mazauna yankin Komatipoort da ke daura da gandun dajin Mpumalanga da su lura da kyau wajen zirga-zirgarsu saboda tserewar da wasu zakuna biyar suka yi daga gandun namun daji na Kruger National Park.
An dai yi amanna zakunan suna ta walagigi a yankin da ke kusa da gandun namun dajin a ranar Talata 9 ga watan Mayu, kamar yadda gidan rediyon BBC Hausa ta ruwaito.
KU KARANTA: ‘Dalilin daya sa aka ga yan matan Chibok ɓul-ɓul’ – Fadar shugaban kasa
Sai dai hukumar gandun namun dajin ta ce tuni an gano wajen da zakunan suke a can kusa da kan iyakar kasar Swaziland, bayan da aka yi amfani da helikwafta don a gano inda zakunan suke.
Da fari dai mahukuntan gandun dabbobin sun bayyana cewar Zakunan sun watsu inda suka rabu akan hanya, ana ma zaton sun kashe wata saniya, don haka ake gargadin jama’a da kada su tsaya daukan hotuna da su, saboda hatsarinsu.
A yanzu masu kula da gandun namun dajin suna kokarin kama su don harba musu allurar kashe jiki don su samu damar mayar da su cikin gandun.
Majiyar Legit.ng tace mutane sun samu kwanciyar hankali sosai bayan da aka gano inda zakunan suke, kuma ba a samu rahoton cewa sun yi wa kowa illa ba.
Wani mazaunin yankin ya ce ya ga zakunan a ranar Litinin da daddare amma sa'arsa daya yana cikin mota ne ba da kafa yake tafiya ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga wasu hanyoyin tsimin kudi musamman a halin matsin tattalin arziki
Asali: Legit.ng