Kasar Iran zata yi luguden wuta a Saudiyya, amma banda Ka’aba da Masallatai
-Tsananin karancin jituwa tsakanin Saudiyya da Iran ya dauki sabon salo
-Kasar Iran tace muddin Saudiya tayi ba daidai ba zata ga ba daidai ba
Ministan tsaro na kasar Iran Huseyin Dehkan ya bayyana cewa, da zarar hukumomin Saudiyya sun takale su fada da sojoji to su ma za su yi wa kasar luguden wuta amma ban da wurare masu tsarki.
Gidan jaridar Turkiyya ta ruwaito Dehkan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da kafar talabijin ta Al-Manar da ke Labanan inda ya gargadi Saudiyya game da batun kai wa Iran hari inda ya ce:
KU KARANTA: ‘Dalilin daya sa aka ga yan matan Chibok ɓul-ɓul’ – Fadar shugaban kasa
"Idan Saudiyya ta yi wautar kai wa Iran hari soji, to Iran din za su yi wa kasar luguden wuta amma ban da garuruwan Makka da Madina."
Dehkan ya cigaba da fadin “Don suna ganin suna da kwararrun sojojin sama ne suke yin baki, toh mu zuba mu gani.”
Kakakin Rundunar Sojin Iran Janaral Sayyid Msud Jaza'iri ya bayyana cewa, Iran ba ta tsoron wasu kasashe kanan da suke gabas ta tsakiya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Jaza'iri ya ce, Saudiyya ta zamo karen farautar Yahudawa da Amurka musamman a wajen kuntata wa kasashen Musulmi tare da haddasa fitintinu.
A wata tattauna wa da Ministan tsaro na Saudiyya Muhammad Bin Salman yayi da manema labaru a makon data gabata yace, zasu mayar da hankali wajen yakar Iran, yace zasu kai musu yaki har gida.
“Mun san mun tsole ma Saudiya Ido, don haka ba zamu jira har sai yaki ya tarar damu a Saudiya ba, amma zamu dage mu kai musu yakin har gida.” Inji Muhammad Bin Salman.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Amurka tayi barazanar kai harin bom kasar Syria
Asali: Legit.ng