Wani fitaccen dan fim din Hausa na neman taimakon ‘yan Najeriya da gaggawa (Hotuna)
- Iyalan fitaccen dan fim din Hausa nan wato Malam Waragis na bukatar tallafi daga ‘yan Najeriya kan ciwon koda da Malam Waragis ke fama da ita a yanzu
- Fitaccen mawakin finafinan Hausa Sa'eed Nagudu ya ziyarci marasa lafiyar inda ya baiwa iyalansa gudummawar kayan masarufi da kuma kudi
Iyalan fitaccen dan fim din Hausan nan Malam Muhammad Umar wanda aka fi sani da Malam Waragis sun bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin wadataccen kudin da za su ci gaba da jinyarsa a asibiti.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, an kwantar da Malam Waragis ne a wani asibiti dake garin Jos sakamakon ciwon koda da yake fama da ita a yanzu haka.
A yayin tattaki tun daga Kano domin duba lafiyar Malam Waragis da ya yi, fitaccen mawakin finafinan Hausa Sa'eed Nagudu ya baiwa iyalansa gudummawar kayan masarufi da kuma kudi, inda kuma ya yi fatan Allah ya tashi kafadun mara lafiyan.
Iyalan mara lafiyan sun mika godiyarsu ga dimbin jama'ar da suka bada gudummawa ta hanyar bada tallafin kudi da kuma masu yi wa mara lafiyan addu'ar samun lafiya.
KU KARANTA KUMA: Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau
Har yansu dai kofa a bude take ga masu bukatar tallafawa Malam Waragis kasancewar ba su da isasshen kudin da za a yi jinyar nasa a asibiti.
Ga duk mai bukatar taimakawa Malam Waragis, ga account number na dansa
BANK: First Bank
ACC Number: 3071453500
NAME: Ibrahim Muhammad Ummar
Domin karin bayani za a iya tuntubar dan Malam Waragis, wato Ibrahim ta wannan lamba 0814 856 0384
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ku kali farashin kayan masarufi a kasuwanni
Asali: Legit.ng