Ku sadu da yaron da ya fara shan shigari tun yana dan wata 18 (Hotuna)

Ku sadu da yaron da ya fara shan shigari tun yana dan wata 18 (Hotuna)

- Ardi Rizal, da ne ga Diana Da Mohammad da ke zaune a wani kauye a yankin Sumatra na kasar Indonesia.

- Yaran ya fara shan tabar sigari tun a lokacin da yake dan watanni 18 a lokacin da mahaifinsa Mohammad ya dandana masa.

- Yayin da ya cika shekaru biyu, Ardi ya kan sha tabar sigari akalla 40 a kowacce rana.

Legit.ng ta samu cewa labarin Ardi ya ja hankalin duniya a lokacin da aka sanya hotunansa ya na zukar taba sigari a shafukan Internet a shekarar 2010, a lokacin Ardi yana mai shekaru biyu.

Har sai da ta kai Hukumomi a garin sun yi wa iyayen Ardi alkawarin mota idan har ya daina shan sigari, al’amarin da ya gagara saboda yadda ya ke ihu da kuka da korafin cewa ya na jin jiri idan aka hana shi.

Ku sadu da yaron da ya fara shan shigari tun yana dan wata 18 (Hotuna)
Ku sadu da yaron da ya fara shan shigari tun yana dan wata 18 (Hotuna)

KU KARANTA: An kama wani mutum da soyayyun sassan mutum

Saboda illar da sigari ta yi masa, ko iya gudu ba ya yi a cikin ‘yan uwansa yara, kullum ya na jibge a guri daya.

A wanna shekara Ardi ya cika shekaru 9. Tuni iyayen sa suka yi nasarar rabashi da tabar sigari tare da hadin gwiwar gwamnati da masana a fannin lafiya.

A lokacin da ya daina shan sigari, ya na mai shekaru 5, sai ya mayar da soyayyar da yake yi mata kan abinci, lamarin da ya sa ya kamu da cutar tsananin kiba.

An sha fama kafin a iya raba Ardi da cin abincin da ya wuce kima, inda yanzu haka ya samu cikakkiyar lafiya, kuma yana rayuwar sa kamar sauran yara sa’anninsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng