Rashin lafiyar Buhari: Wani mai maganin gargajiya ya bukaci a bashi dama

Rashin lafiyar Buhari: Wani mai maganin gargajiya ya bukaci a bashi dama

- Wani shahararren mai maganin gargajiya a garin Kano mai suna Abdulhameed Qaseem dake a karamar hukumar Gwale ya bukaci a bashi dama domin ya ba Buhari irin magungunan sa.

- Yace maganin sa na aiki kamar yankan wuka

Wani shahararren mai maganin gargajiya a garin Kano mai suna Abdulhameed Qaseem dake a karamar hukumar Gwale ya bukaci a bashi dama domin ya ba Buhari irin magungunan sa.

Shahararren mai maganin ya bayyana cewa hakika ya damu da halin da Buharin yake ciki musamman ma na jinyar da yake ta sha don haka ne ma ya yanke shawarar taimaka masa da maganin kyauta.

Rashin lafiyar Buhari: Wani mai maganin gargajiya ya bukaci a bashi dama
Rashin lafiyar Buhari: Wani mai maganin gargajiya ya bukaci a bashi dama

KU KARANTA: An gano warin kaji na maganin cizon sauro

Legit.ng ta samu labarin cewa a cewar sa: "Hakika na damu matuka da rashin lafiyar ta Buhari amma ni na sha alwashin taimaka masa da irin maganin mu na gargajiya."

Mai maganin ya ci gaba da cewa ya gaji magungunan sa ne daga wurin mahaifin sa sannan kuma mutane da dama sun gwada kuma sun samu sauki sosai.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng