Marubuci ya kafa tarihi yayin daya rubuta Qur’ani da yafi tsawo a duniya (Hotuna)
-Marubuci dan kasar Misra ya katabta Al-Qur'ani cikin wani salo dayake bako ga mutane
-Saad ya rubuta Qur'ani a shafi daya da tsawonsa ya kai mita 700
Wani mutum balaraben kasar Misra ya kafa tarihi yayin daya rubuta Qur’ani bugun hannu a shafi guda da tsawonsa ya kai mita 700 a shekaru uku cur.
Wannan mutum mai suna Saad Mohammed kwararre ne a harkar rubuce rubuce da zane zane masu kayatarwa, kamar yadda ya kawace dakinsa da zane zane daban daban yace:
KU KARANTA: Kwankwaso ya soki lamirin yansanda na kai farmaki gidan dan uwansa
“Tsayin Qur’anin nan ya kai mita dari bakwai, kuma da kudina nayi shi, duk da cewa dai ni ba mai kudi bane, kuma bani da wata kadara.” Inji shi.
Legit.ng ta ruwaito Muhammed na kokarin aika Qur’anin nasa ga hukumuar kundin tarihin duniya don ya kafa tarihin rubuta Qur’anin da yafi tsawo a duniya gaba daya, don haka yana neman taimako daga gwamnati ko jama’a gama gari don samun daman shiga kundin tarihin.
Ga sauran hotunan nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda sunan Allah ya bayyana a jikin bishiya, kalla
Asali: Legit.ng