Za'a kashe wasu barayin shanaye 3 ta hanyar rataya

Za'a kashe wasu barayin shanaye 3 ta hanyar rataya

- Anyanke musu hukuncin ne bayan Mai shari'ar Jastis Josiah Majebi ya same su da sata tare da kisan gilla da suka yiwa manomi a jihar Kogi

- A cewarsu, Yusuf, Ado da shugabansu, Agwaijo mun hadu muka tanaji adduna ne domin tunkarar mai shanayen

Wata babbar kotu a kogi dake garin okene a ranar alhamis ta yankewa makiwata shanaye masu yawo, Muhammed Lawal Jauro da Yusuf Sanni, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A nyanke musu hukuncin ne bayan Mai shari'ar Justice Josiah Majebi ya samesu da sata tareda kisan gilla da sukayi.

An kamasu da manya-manyan laifuka-makirci, fashi,da kisan gilla wadanda suka samawa hakkokin zamantakewa. a wata majiyar na Legit.ng ta samo cewa an sanar da kotun a watan Janairu 2016,cewa Dauda Abdullahi ya bada rahoto gameda mumunar kisa da satan shanaye da akayiwa Haruna,a wani yankin gonakin da ke Okene.

Ya kara da cewa bayan bincike, an cafke wasu daga masu wannan aika-aikan a Ajase-Ipo a Jihar Kwara tareda shugabansu.

A cigaban bincike Legit.ng ta nakalto cewa an bada takardun rahotanni dake nuna yan aika-aikan sun amsa laifurfukansu bayan musanta tuhumar da ake musu a da.

Daga rahotannin Jauro ya tabbatarda a Disamba, 2015, daya daga abokansa, Yusuf, mazaunin Kabba junction, Zariagi, ya kirashi a waya kuma ya sanardashi gameda wasu shanaye mallakar Haruna,a wani daji a Okene.ya basa shawarar suje domin su sace wadannan shanayen. Bayan haka shugabansu Agwaijo Wetti, mazaunin kauyen Tyre a hanyar Okene-Auchi,ya bada Umarnin su hadu a wani daji a kusa da gurin.

KU KARANTA: Dalilin da ya hana Shugaba Buhari halartar taron FEC – Lai Mohammed

A cewarsa: ''Ni, Yusuf, da Ado da shugaban namu, Agwaijo mun hadu muka tanaji adduna domin tunkarar mai shanayen nan, a nan ne muka farmasa da sara muka kaishi har lahira sannan muka kora shanayen nasa zuwa Ajase-Ipo a jihar Kwara.''

A shari'ar mai Shari'a, Justice Majebi ya nuna cewa tabbas wanna laifukkan nasu dukda ikirari masu matukar nauyi ne kuma suna tabbatar da aukuwar hukunci akansu,kautar da hukunci akansu don tausasawa abune da kin yuwuwarsa keda wahala. a karshe dai ya yankewa kowannensu hukuncin shekaru 28 akan laifuka uku, sannan kuma Rataya a sakamkon kisan gillan da sukayi.

Ku biyomu ta facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko ta twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng