Kalmomin yorubanci 10 masu alaka da Larabci

Kalmomin yorubanci 10 masu alaka da Larabci

- Kalmomin yorubanci masu alaka da harshen larabci

- Akwai kalmomin yorubancin da dama da ake amfani da su wanda aka samu daga kalmar larabci

Harshen yorubanci wanda ke dauke da rinjayi harshen larabci kuma akwai da yawa daga kalmomin da muke amfani da kowace rana wanda yana da alaka da yorubanci.

Legit.ng ta tattaro wasu kalmomin yorubanci masu alaka da harshen larabci mai yiwuwa ba a sani ba.

1. Wahala

'Wahala' na nufin matsala a yorubance, an samu daga kalmar larabci "wahla," wanda yake nufin "tsoro," ko "ta'addanci."

2. Iwaju

'Iwaju' na nufin gaba a yorubance, an samu kalmar ne daga Larabci "al-wajh," wanda yake nufin "gaba" ko "fuska."

3. Faari

'Faari' na nufin takama a yorubance, an samu kalmar ne daga Larabci "Fakhr," wanda yake nufin "girma" ko "girman kai".

4. Barika

'Barika' na nufin taya murna a yorubance, an samu kalmar ne daga Larabci "al-Baraka," wanda yake nufin "gaisuwa." Ko "albarka"

5. Asiri

'Asiri' na nufin asirce a yorubance, an samu kalmar ne daga larabci "as-sirr" inda shi ma yana nufin asiri

6. Ara

'Ara' yana nufin tsawa a yorubance, an samu daga kalmar larabci "ar-ra'd.

KU KARANTA KUMA: Za'a dauki malaman makaranta 1,000 a wannan jihar ta Arewa

7. Abere

'Abere' na nufin allura, an samu daga kalmar larabci "ai-bra," wanda kuma na nufi allura.

8. Adura

Adura a yorubance na nufin sallah, an samu daga kalmar larabci "du'a," wanda kuma na nufi sallah

9. Fitila

Wannan yana nufin fitila a yorubance, an samu ne daga kalmar larabci, "fatil".

10. Alubosa

Wannan na nufin albasa a yorubance, an samu daga kalmar larabci, "Al-basal"

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wata yar Najeriya mai ganguna da hannuwanta da kafafunta da kuma kanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng