Kisan Sheikh Ja’afar: Shekarau ya bai wa ‘yansanda wa’adin kwanaki 14 su wanke shi

Kisan Sheikh Ja’afar: Shekarau ya bai wa ‘yansanda wa’adin kwanaki 14 su wanke shi

-Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya musanta zargin hannu a kisan sheikh Ja'afar

-Shekarau ya baiwa hukumar yansandan Najeriya kwanaki 14 su wanke shi daga zargin

Tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bai wa Sufeto Janar na Yan sandan kasar nan kwanaki 14 don ya wanke shi daga zargin takardar da suka ce tana alakanta shi da kashe Sheikh Jaafar Adam ko kuma ya gurfanar dasu gaban kotu.

Gidan rediyon Faransa ta ruwaito cikin wata wasika da Ibrahim Shekarau ya sanyawa hannu, ya bukaci Sufeto Janar din ya fito fili ya yiwa ‘Yan Najeriya bayani kan abinda takardar da ake zargi ta kun sa.

KU KARANTA: Wani mutum yayi wa ɗan achaɓa yankan rago a Katsina

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa Shekarau ya sake bukatan Sufeton yansandan da yayi bayani kan bambamcin binciken da hukumar yansandan tayi a karkashin Hafiz Ringim wanda DIG Emmanuel Ojukwu ya shaidawa duniya, da kuma wanda suke zarginsa.

Kisan Sheikh Ja’afar: Shekarau ya bai wa ‘yansanda wa’adin kwanaki 14 su wanke shi
Shekarau

Shekarau ya ce yin karin haske kan takardar na da matukar tasiri a gare shi da daukacin magoya bayan sa.

Kimanin sati biyu da suka gabata ne jami'an yansanda suka ce sun gano wata takarda kan yadda Malam Ibrahim Shekarau ya tsara kisan sheikh Ja'afar a gidan Sanata Danjuma Goje.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kaga mutumin dake kokarin kawo zaman lafiya a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel