Wani mutum yayi wa ɗan achaɓa yankan rago a Katsina

Wani mutum yayi wa ɗan achaɓa yankan rago a Katsina

-Wani mugun mutumi ya hallaka dan achaba ya sace babur dinsa

-Mutumin yace dalilin kashe dan achaban shine saboda bashi da kudin biyansa

Dubun wani da ake zargi da daukar yan acahaba haya yana kashesu ta cika, bayan da aka kama shi a lokacin da yayi ma wani dan achaba yankan rago.

Shi dai wannan mugum mutum mai suna Isiya Inusa mai kimanin shekaru 40 ya shiga hannun jami’an hukumar yansandan jihar Katsina ne a ranar Alhamis data gabata, inda yace ya kashe dan achabar ne saboda ba zai iya biyansa kudin aikinsa naira dari ba.

KU KARANTA: Jerin kamfanunuwa 5 da suka baiwa Babachir cin hancin naira miliyan 507

Isiya ya bayyana cewar ya dauko dan achabar ne daga Kankara zuwa kauyen Kabuke “A hanyar mu ta zuwa , a daidai rafin makwanci na yanka shin a tafi da babur din na boye a gidan wani mutum dana amince da shi.”

Wani mutum yayi wa ɗan achaɓa yankan rago a Katsina
Isiya Inusa tare da babur din Alhassan

Dayake bayanin dalilin wannan aika aika, Isiya yace “Na hau babur dinne bani da kudin da zan biya shi idan mun isa, kuma naira dari yace in biya, shi yasa na aikata haka.”

Sai dai Isiya ya nemi amai afuwa da sassauci, inda ya bukaci a kais hi gidan wanda ya kashe ya cigaba da yi ma iyayensa hidima tamkar dansu.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar wannan shine karo na uku da Isiya ke aikata wannan aika aika akan yan achaba. Daga karshe hukumar yansanda ta bayyana sunan mamacin da Al-Hassan Husaini, mai shekaru 43.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani hukunci ya dace da barayin gwamnati?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng