Alhamdulillah: Najeriya ta ƙirkiro maganin warkar da cutar farfaɗiya

Alhamdulillah: Najeriya ta ƙirkiro maganin warkar da cutar farfaɗiya

-Kwararru yan Najeriya sun samar da maganin cutar farfadiya

-Ministan kimiyy da fasaha Ogbonnaya Onu ya shawarci yan Najeriya su siya

Ma’aikatar kimiyya da fasaha ta sanar da cewa tana gab da kammala shirin kirkiro maganin cutar farfadiya a Najeriya, inji rahoton jaridar Premium Times Hausa.

Ministan kimiya da fasaha Ogbonnaya Onu ne ya bayyana hakan a taron bita da ma’aikatarsa ta shirya wa yan Najeriya a babbar birnin kasar Amurka wato New York.

KU KU KARANTA: Obasanjo ya tsine ma duk masu yi ma gwamantin Buhari zagon ƙasa

Ministan ya kara da cewa a yanzu hakan sun gama yi wa maganin duka gwaje-gwajen da ya kamata domi hakamsuna jiran hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa Najeriya NAFDAC ta yi nata gwajin akan maganin kafin su kammala sauran abin da ya kamata.

Alhamdulillah: Najeriya ta ƙirkiro maganin warkar da cutar farfaɗiya
Kwararru a bakin aiki

Majiyar Legit.ng ta jiyo minista Onu yana fadin “Muna kokarin kirkiro maganin warkar da cutar farfadiya kuma mun gwada ingancinsa. A yanzu muna jiran hukumar NAFDAC ta kammala nata gwajin akan maganin ne.’’

Alhamdulillah: Najeriya ta ƙirkiro maganin warkar da cutar farfaɗiya
Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu

“ kamar yadda aka sani cewa cutar farfadiya cutace wanda ta adabi kowa a duniya saboda hakan ya kamata mu hada hannu gaba daya wajen siyar da maganin.” Inji Onu

Onu ya yi kira ga mutanen Najeriya mazauna kasar Amurka dasu taya Najeriya wajen tallata maganin a can Amurka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli mutumin dayafi karfi a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng