Rikicin ƙabilanci ya kaure a jihar Filato, Sojoji sun shiga tsakani
-Saura kiris da an samu mummunan rikici tsakani wasu kabilu dake kiyayya da juna
-Kabilun kuwa sune kabilar Afizere da kabilar Anaguta na jihar Filato
Rikicin kabilanci ya kaure tsakanin kabilar Afizere da kabilar Anagura dake karamae hukumar Jos ta Arewa na jihar Filato a ranar Talata 2 ga watan Mayu.
Sai dai sojoji na musamman dake tabbatar da zaman lafiya a jihar Filati, Operation Safe Haven, sunyi gaggawan kai dauki, inda suka samu nasarar dakile rikicin daga munana.
KU KARANTA: An yi gudun famfalaki yayin da wata gawa tayi wuf! ta kamo hannu dan uwanta a Filato
Jaridar Vanguard ta ruwaito rikicin ya faro ne daga Anguwan Rukuba, lokacin da wasu matasan kabilar Afizere suka cire wani shaida da kabilar Anaguta ta jibge a gefen hanya wanda ke nuni da gidan shugaban su.
Wannan ne ya harzuka kabilar Afizere, inda dukkanin kabilun suka harzuka, kowa ya fidda makamai, daba don zuwan dakarun rundunar sojin kasa ba, da labara ya sha bambam.
Amma a yanzu komai ya lafa, kuma kowa ya koma bakin aikinsa, kamar ba’a yi ba, inji majiyar Legit.ng
Majiyar ta bayyana cewar an girke dakarun soji da dama suna gudanar da sintiri a yankin don kare sake afkuwan wani rikicin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda Sojoji ke horar da Boko Haram
Asali: Legit.ng