Bahubali 2: Fin din Indiya da ya kafa muhimmin tarihi a duniya

Bahubali 2: Fin din Indiya da ya kafa muhimmin tarihi a duniya

- Yau ne rana ta hudu da aka fara nuna fim din Bahubali na biyu a gidajen kallo a fadin duniya kuma tuni fim din ya kere kowanne fim da aka taba yi a masana’antar Bollywood karbuwa a gurin jama’a

- Izuwa jiya, rana ta uku da aka fara nuna fim din, ya samu fiye da Biliyan 5 na kudaden indiya, wanda babu wani fim da ya taba samun wannan nasara, kuma a kankanin lokaci irin wannan

Legit.ng ta samu labarin cewa Bahubali na daya ya fito ne a shekarar 2015, kuma shi ma ya samu karbuwa. Amma tuni na biyun ya kaure shi da kaso 350 bisa dari.

Dumbin mutane ne ke ta kwarara sinimomi a fadin duniya domin su kalli wannan fim da ya bayar da labarin sarauta.

Bahubali 2: Fin din Indiya da ya kafa muhimmin tarihi a duniya
Bahubali 2: Fin din Indiya da ya kafa muhimmin tarihi a duniya

KU KARANTA: Rikici a jam'iyyar APC ta Katsina

Ko a kasar Amurka, Bahubali ya kaure sabon fim din Fast and Furious 8 a gida na farko.

Kamar yadda majiyar mu ta Alumma ta bayyana, a Kano ana nuna fim din a Film House Cinema da ke Ado Bayero mall a ranakun Juma’a zuwa Alhamis da karfe 1:00 na rana da 4:30 na yamma da 8:00 na dare.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon shahararren mawakin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel