Musulunci ya samu gagarumar nasara a jihar Neja (Hotuna)

Musulunci ya samu gagarumar nasara a jihar Neja (Hotuna)

- Yan kabilar Kambari sama da 400 ne suka karbi addinin musulunci

- Yan yankin Warari da ke karamar hukumar Rijau a Jihar Neja

- Sun anshi mulkin ne ta hannun kungiyar 'Initiative For Muslim Women Of Nigeria'.

Yan kabilar Kambari sama da 400 ne suka karbi addinin musulunci a yankin Warari da ke karamar hukumar Rijau a Jihar Neja a karshen makon nan ta hannun kungiyar 'Initiative For Muslim Women Of Nigeria'.

Bayan dawa'a da kai kayan tallafi da kungiyar ta yi, bisa jagorancin Malama Rabi´ah Sufyan Ahmad.

Legit.ng ta samu labarin cewa a wani labarin kuma, musulunci ya karbi bakuncin wani bawan Allah a Jami'ar Bayero da ke Kano karkashin jagorancin shugabancin Kungiyar Dalibai Musulmi ta kasa reshen Jami'ar (MSSN).

Musulunci ya samu gagarumar nasara a jihar Neja (Hotuna)
Musulunci ya samu gagarumar nasara a jihar Neja (Hotuna)

KU KARANTA: Ana sa ran faduwar Dala a yau

Bawan Allah mai suna Jimoh da farko, ya koma Aliyu bayan ya karbi kalmar shahadar shiga Musulunci.

Aliyu wanda dan asalin kasar Togo ne ya nuna sha'awarsa ta shiga Musulunci bayan ya fahimci cewa Musulunci shine Addinin gaskiya. Inji shi

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng