Kun ga jihohin Najeriya 11 dake cin amanar Shugaba Buhari (Jerin Sunaye)

Kun ga jihohin Najeriya 11 dake cin amanar Shugaba Buhari (Jerin Sunaye)

- A yau ne ma'aikata da 'yan kwadago a duk fadin duniya ke bikin ranar ma'aikata ta duniya.

- An zabi ranar daya ga kowanne watan Mayu domin bikin zagayowar wannan rana saboda tunawa da kisan wasu ma'aikata hudu da 'yan sanda suka yi a birnin Chigaco na Amurka a shekarar 1886, yayin wani yajin aiki.

A irin wannan rana ne ma'aikata ke la'akari da irin gudunmuwar da su ke bayar wa wajen cigaban tattalin arzikin kasar da suke.

Kamar sauran kasashen duniya, Najeriya ma na daga cikin kasashen da ke gudanar da wannan biki na ranar ma'aikata.

Comrade Ayuba Wabba, shi ne shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC, ya shaidawa majiyar mu cewa, suna tuna wannan rana ne da taken, gudunmuwar da ma'aikata ke bayarwa wajen cigaban kasa, musamman a irin yanayin da kasar ke ciki a yanzu.

Legit.ng ta tsinkayi Comrade Wabba, yana cewa ma'aikata su ne suka fi kowa shan wahala a irin yanayin da Najeriya ke ciki a yanzu.

Saboda a cewarsa, akwai jihohi kusan goma sha daya da basa biyan albashi da biyan 'yan fansho hakkokinsu.

Kun ga jihohin Najeriya 11 dake cin amanar Shugaba Buhari (Jerin Sunaye)
Kun ga jihohin Najeriya 11 dake cin amanar Shugaba Buhari (Jerin Sunaye)

KU KARANTA: Wai ance Buhari baya iya cin abinci

Shugaban kungiyar ta kwadago, ya ce za a gudanar da irin wannan biki a dukkanin jihohin Najeriya banda jihar Kogi kadai.

Comrade Wabba,ya cigaba da cewa, a wannan rana sun gayyao shugaban kasa da kuma 'yan majalisu, in da za a gudanar da jawabai.

Sannan kuma ya ce abinda ma'aikata ke so a yanzu shi ne, kasancewar cin hanci da rashawa ya yiwa kasar katutu, to yanzu duk wanda zai bayar da bayani a kan kamo wani wanda ya saci kudin gwamnati, to ya kamata a samar da dokar da zata bashi kariya.

Kuma idan har an samu mutum da laifin satar kudin gwamnatin, to yakamata a cikin lokacin kankani a hukunta shi.

Daga bisani, ya yi tsokaci a kan jihohin da ba sa biyan albashi, inda ya ce duk jihohin da basa biyan albashi to ba mamaki ko sun ciwo bashin da ya fi karfinsu, ko kuma sun yi kwangiloli na bogi domin ayi almubazzaranci da kudaden jama'a.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng