Kisan Sheikh Ja'afar: Shekarau yace zai iya zuwa kotu
- Tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yana bin kadin ɓata-suna da 'yan sandan ƙasar suka yi masa.
- Rundunar 'yan sandan ta ce ta gano wata takarda da ke alaƙanta Shekarau da kashe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam.
A cewarta jami'anta ne suka gano takardar bayan wani samame da suka kai gidan sanata Danjuma Goje a Abuja.
Mai magana da yawun Shekarau, Malam Sule Ya'u Sule ya ce ba shakka suna bin bahasin wannan batu a wajen 'yan sanda.
Legit.ng ta samu labarin ya ce sun tuntuɓi 'yan sanda a kan su fito su binciko gaskiyar wannan al'amari kuma su yi wa jama'a bayani.
Sule Ya'u Sule ya ce suna iya zuwa kotu a kan wannan ɓata-suna da ya ce an yi wa Ibrahim Shekarau.
A cewarsa, takardar da 'yan sanda suka yi iƙirarin sun gano a gidan Sanata Danjuma Goje tsohuwar takarda ce da wasu abokan hamayya suka rubuta don shafa wa Shekarau kashin kaji.
Ya ce "Ni ma ina da wannan takarda. Al'umma da yawa a Kano sun samu wannan takarda...Na tabbata wannan takarda ce wannan tsohon gwamna (sanata Danjuma Goje) ya samu. Idan kuma wata ce daban, ya kamata 'yan sanda su fito su yi wa mutane bayani."
KU KARANTA: An fallasa albashin Sarkin Kano
Shi da kansa Malam Ibrahim Shekarau ne a wancan lokaci ya nemi 'yan sanda su yi bincike a kan wannan takarda.
A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ja'afar Mahmud Adam yayin sallar asubah a Kano.
Mai magana da yawun Shekarau ya ce 'yan sandan sun yi bincike a kai kuma sun san abin da suka gano game da batun, don haka ya kamata su fito su yi wa al'umma bayani.
Da aka tambaye shi ko Shekarau zai ɗauki matakin shari'ah a kan wannan al'amari, ya ce suna jiran bayanin 'yan sanda kafin su san mataki na gaba da za su ɗauka.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng